in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin sama na kasar Sin za su ci gaba da neman jirgin saman Malaysia da ya bace
2014-04-05 16:32:11 cri
Kakakin sojojin sama na kasar Sin Shen Jinke ya bayyana a ran 4 ga wata a nan birnin Beijing cewa, duk da cewar, ana fuskantar mawuyacin hali wajen neman jirgin saman Malaysia da ya bace, amma sojojin saman kasar Sin na iyakacin kokarinsu kuma zasu ci gaba da yin hadin gwiwa da sauran bangarorin dake aikin bincike da ceto na kasa da kasa domin neman wannan jirgi. A ranar 4 ga wata kuma, an sake tura jirgin sama daya daga filin saukar jiragen sama na Perth na kasar Austriliya zuwa sararin ruwan tekun dake arewa maso yamamcin Perth domin gudanar da bincike a wannan wuri.

A cewar Mr Shen, sojojin sama na kasar Sin suna bin umurnin kasa yadda ya kamata, kuma suna iyakacin kokarinsu.

Tun ranar 8 ga watan Maris, an tura jiragen sama da dama domin neman wannan jirgi. Ban da jirgin sama samfurin IL-76, akwai jiragen sama iri-iri na kasar Sin dake gudanar da aikinsu a wurare da dama. Jirgin sama Y-8 da Sin ta kera yana gudanar da aiki a Malaysia, tare da bada babban taimako. Haka kuma jirgin sama Y-20 kirar kasar Sin, bayan an cimma nasarar aikin gwajinsa na farko, ana sa ran ganin zai taka muhimmiyar rawa wajen tinkarar bala'u da gudanar da aikin ceto har ma da ba da tallafin jin kai da sauransu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China