A cewar Firaministan kasar ta Austreliya Tony Abbott, tsohon jami'in rindunar sojin saman kasar Angus Houston ne zai jagoranci cibiyar ta hadin gwiwa da akaiwa lakabi da JACC mai sansani a Perth.
Ana sa ran dai wannan cibiya, zata dauki nauyin kula, tare da aiwatar da tallafin gwamnatoci, a aikin laluben wannan jirgi da ake ci gaba da yi yanzu haka. Haka zalika, cibiyar zata yi aiki kafada da kafada, da daukacin masu ruwa da tsaki, ciki hadda 'yan uwa da iyalan fasinjojin dake jirgin, da kuma 'yan jaridar kasa da kasa.
Kawo yanzu dai jiragen saman kasashen Austreliya, da Sin, da Japan, da na Malashiya na ci gaba da neman baraguzan jirgin da ake zaton ya fadi a yamma da gabar ruwan birnin Perth na yammacin Australiya. Sauran kasashen dake tallafawa aikin sun hada da New Zealand, da Koriya ta Kudu da kuma kasar Amurka.(Saminu Alhassan)