in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin jiragen sama na Malaysia ya tabbatar da cewa, babu wanda ya tsira daga jirgin da ya bace
2014-03-25 16:45:48 cri

A ranar 25 ga wata bisa agogon wurin, kamfanin jiragen sama na kasar Malaysia ya shirya wani taron manema labaru a filin jiragen sama na kasa da kasa da ke birnin Kuala Lumpur, inda shugaban kamfanin Tan Sri Md Nor Yusof ya bayyana cewa, shaidar da ta tabbatar da faduwar jirgin sama ita ce, wurin da aka rasa duriyar jirgin saman a karshe shi ne kudancin ruwan tekun India dake nesa da doron kasa, saboda haka babu babu yiwuwar jirgin ya sauka.

A tsawon kusan awa daya na taron manema labaru, darektan zartaswa na kamfanin jiragen sama na Malaysia Ahmad Jauhari Yahya ya bayyana cewa, bisa sabon bayanin da ya samu, an tabbatar da cewa, jirgin ya fada cikin teku, kuma daga ma'aikatan jirgin har zuwa fasinjoji da ke cikin jirgin babu wanda ya tsirar da ransa.

Ya kara da cewa, har yanzu ana bincike, kuma matsalar gudanar da binciken da lokacin da za a kashe za su wuce tunanin jama'a, kamfaninsa zai biya diyya ga iyalan ma'aikata da fasinjojin jirgin tare da yi masu adu'a. Sai dai kuma kamfanin bai fayyace ci gaba da aka samu daga binciken ba, domin kaucewa yin hasashe ko kadan dangane da wannan lamari. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China