Mataimakin firaministan Australia Warren Truss ya bayyana a yau cewa, ya zuwa yanzu jiragen sama na Australia, da na Amurka, da na New Zealand suna neman jirgin saman a wannan yankin teku, yayin da jiragen sama na Sin da na Japan za su isa a gobe. Ya ce, jiragen sama na gudanar da aikin bincike na awa biyu-biyu. Ban da jiragen saman soja kuma, jiragen saman fasinja su ma sun fara shiga wannan aiki.
Shugaban rukunin ba da jaroganci ga rundunar sojan sama ta Sin, Liu Dianjun ya bayyana cewa, yau jiragen saman soja na Sin za su tashi zuwa Australia domin gudanar da aikin bincike.
An samu labari daga ofishin jakadancin Sin a Australia cewa, jirgin ruwan nazari kan kimiyya na Sin mai suna Xuelong ya riga ya tashi zuwa wannan yankin teku da aka gano tarkacen da ake tsammanin na jirgin da ya bace ne a jiya 21 ga wata, an kiyasta cewa, shi zai isa a ranar 25 ga wata.
Jiragen ruwa guda hudu na ma'aikatar sufuri ta Sin suna gudanar da bincike a yankin teku dake yamma da kasar Indonesia bisa sabon shirin bincike, kuma za su ci gaba da aikin zuwa kudancin tekun India. A sa'i daya, jiragen ruwan soja na Sin su ma suna isa wannan yankin teku.
Cibiyar aikin ceto da bincike a yankin teku ta Sin ta riga ta bukaci jiragen ruwa na kamfanin COSCO da na China Shipping zuwa wannan yankin teku domin gudanar da aikin bincike.(Fatima)