A lokacin zantawar su Mr Li Keqiang ya nuna cewa, ya zuwa yanzu, aikin da aka sa gaba shi ne aikin ceto, jiragen ruwa da suka kware a fannin aikin ceto fiye da goma na kasar Sin suna kokarin gudanar da aikinsu a sararin teku, kuma gwamnatin kasar Sin na bukatar jiragen ruwan na haya da za su zarce wadannan yankuna su ba da gudunmawa wajen gano wannan jirgin.
Ban da haka, a cewarsa, Sin ta tura jiragen sama da dama da tauraron Bil Adam 21 domin gano inda wannan jirgi yake. Baya ga wannan kuma, Sin ta sanar da halin da ake ciki ga kasashe 25 tare kuma da nemansu da su ba da taimako.
Ya jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da gudanar da aikin ceto, kuma tana fatan kasar Malaysia za ta gabatar da bayanai da ta tattara cikin lokaci, da gudanar da aikin ceto da bincike kan dalilin aukuwar hadarin tare. Ya ce ya kamata gwamnatin Malaysia da kamfanin jiragen sama na kasar su gudanar da aikinsu yadda ya kamata, da kwantar da hankalin iyalan wadanda ke cikin jirgin da ya bace da suka hadda Sinawa.
A nasa bangare, Najib Tun Razak ya yi bayani kan aikin ceto da kasarsa ta Malaisiya ke yi yanzu da matakan da kasar za ta dauka nan gaba, yana mai cewa, kasar za ta yi iyakacin kokarin gano jirgin tare da ceto mutane da ke ciki. (Amina)