Bisa hasashen da rahoton ya yi, an ce, alkaluman GDP na kasar Sin za su kai dallar Amurka biliyan 33510, adadin ya dara na kasar Amurka na dallar Amurka biliyan 32240.
Haka zalika, rahoton ya kuma nuna cewa, idan aka kwatanta da wasu hasashen da aka yi a baya, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin bai kai saurin da aka taba yin hasashe ba, dalili shi ne, kasar Amurka wadda ita ce kasar da ke kan gaba wajen samun bunkasuwar tattalin arziki cikin yammacin kasashe tana ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arziki a halin yanzu, kana, cikin 'yan shekarun nan, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin bai kai kamar na da ba, sakamakon yanayin karkon bunkasa tattalin arziki a kasar da kuma karuwar adadin tsofaffi cikin al'ummar kasar ta Sin. (Maryam)