An rufe taron tattalin arziki na Kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a ranar Jumma'a 13 ga watan nan, bayan gabatar da manyan bukatun da suka shafi ayyukan raya tattalin arziki na shekara mai zuwa.
Sakon da aka fitar ya kunshi bukatar ci gaba da aiwatar da manufa mai nagarta dangane da hada hadar kudade, da kuma bunkasa manufar bude bakin aljihu, sannan da kara kyautata hanyar da za a bi yayin da ake gudanar da ayyuka daban-daban. Haka zalika sakon ya jaddada wajibcin tabbatar da tanajin isashen hatsi, da dauki matakai iri biyu na yiwa tsare-tsare kwaskwarima, da kuma kandagarkin matsaloli, da shawo kan kalubalen basussukan kananan hukumomi a wurare daban-daban, tare da zurfafa yin kwaskwarima a dukkan fannoni ta yadda jama'a za su ci gajiyar hakan.
Ban da haka, taron ya bayyana a fili cewa, Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufa mai amfani dangane da hada hadar kudi, da kuma manufar kudi ta bude bakin aljihu, da zummar tabbatar da saurin bunkasuwar tattalin arziki, ta yadda za a samar da sakamako mai kyau na zurfafa kwaskwarima.
Wannan manufofi biyu za su kara kwarin gwiwa ga kamfanoni, wajen zuba jari tare da kaucewa haifar da sabbin kalubaloli, matakin da ya dace da halin da ake ciki a halin yanzu.
Dadin dadawa, taron ya jaddada wajibcin fahimtar dangantakar dake tsakanin samun ci gaba mai kyau, da karuwar yawan kayayyaki da za a samar, da kuma samun ingantuwar bunkasuwa mai karko. Haka nan ya dora muhimmanci sosai kan ba da ilmi, da gudanar da jarrabawa, da kuma kyautata tunanin mutane don gane da gudanar da ayyuka yadda ya kamata.
Taron ya kuma sanya aikin samar da isasshen hatsi a sahun gaba a shekarar ta badi, inda aka jaddada wajibcin samar da isashen hatsi da za a iya dogaro da shi. Baya ga wannan, an nemi a warware batun yawan kayayyaki da ake samarwa sama da bukata, inda aka tabbatar da kirkire-kirkire a matsayin hanya daya tilo wadda za a bi.
Gwamnatin kasar Sin dai ta bukaci a kiyaye ikon mallakar fasaha, da sa kaimi ga kyautata manufar buga haraji kan kamfanoni masu kirkire-kirkire. (Amina)