in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Sin ya karu da kashi 7.7 cikin 100 a shekarar 2013
2014-01-20 14:52:09 cri
A ranar 20 ga wata, bisa kididdigar da hukumar kididdigar kasar Sin ta bayar, an ce, a shekarar 2013, yawan kudaden da aka samu daga kayayyakin da aka sayar a cikin a gida ya kai kudin Sin Yuan biliyan 56884.5, abin da ya karu da kashi 7.7 cikin 100, yawan saurin karuwar da aka samu ya yi daidai da na bara.

A gun taron manema labaru da ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta Sin ya shirya, direktan hukumar kididdiga ta kasar Sin Ma Jiantang ya bayyana cewa, a takaice dai, harkokin tattalin arzikin Sin suka gudana yadda ya kamata.

Yawan makamashin da aka yi amfani da shi wajen samun alkaluman GDP na kudin Yuan dubu 10, ya ragu da kashi 3.7 cikin 100, kuma an samu albarkar hatsi a fannin aikin gona, kana an raya harkokin masana'antu da samar da guraben aikin yi yadda ya kamata.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China