A cikin jawabinsa, babban darektan kwamitin tsakiyar JKS, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nazari kan yanayin da ake ciki a fannin tattalin arziki, da waiwaye game da aikin tattalin arziki a shekarar 2013, tare da gabatar da bukatu da manyan ayyuka a wannan fanni a badi. A nasa bangare kuma, firaministan kasar Li Keqiang ya yi jawabi kan manufar tattalin arziki daga manyan fannoni a badi tare da bayyana hakikanan matakan da za a dauka.
Dadin dadawa, a gun taron, an tabbatar da manyan ayyukan tattalin arzikin Sin guda shida da za'a maida hankali a kai a badi, wato ba da tabbaci ga ingancin abinci, kyautata tsarin masana'antu, kula da matsalar basusuka, sa kaimi ga samun bunkasuwa a yankuna cikin daidaito, ba da tabbaci da kyautata rayuwar jama'a, da kuma kara bude kofa ga kasashen waje.(Fatima)