in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin kasar Sin zai samu bunkasuwa yadda ya kamata
2013-12-10 20:31:01 cri
Kamfanin dab'in litattafai na cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewar al'umma ta kasar Sin ta gabatar da takardar bayani kan tattalin arzikin kasar Sin a Talata 10 ga wata, inda ta nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai samun bunkasuwa bisa matsakaicin sauri mai dorewa yadda ya kamata, a sa'i daya kuma Sin za ta kara karfin yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje.

Wannan takardar bayani mai taken "nazari da yin hasashe kan halin tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2014" ta nuna cewa, a cikin wannan shekara da muke ciki, tattalin arzikin kasar Sin ta nuna alamar samun bunkasuwa mai kyau. Daga cikinsu, sana'ar ba da hidima ya samu bunkasuwa fiye da sana'ar masana'antu da kere-kere, farashin kayayyaki zai tashi sannu a hankali bisa tsarin da aka kayyade, ban da haka, an kyautata tsarin kwadago a cikin kasar, sa'an nan kuma kudin shiga da manoma suka samu ya karu fiye da na 'yan birane da garuruwa.

Takardar bayanin ta nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin za ta shiga matakin samun bunkasuwa bisa matsakaicin sauri daga na bisa sauri kwarai, kana yawan karuwa da za a samu a ko wace shekara a fannin mallakar gidaje da gine-gine zai ragu bisa mataki. A cikin shekarar 2014 kuwa, Sin za ta ci gaba da habaka bukatun cikin gida da kuma sa kaimi ga sana'ar kirkire-kirkire, da ba da tabbaci ga samun bunkasuwa bisa jari da za a zuba cikin daidaici, da daga karfin sayayya na jama'a, sannan da ingiza sana'ar kirkire-kirkire, kuma ba za a auna bunkasuwar wani yanki bisa ma'aunin GDP kawai ba.

Dadin dadawa, takardar ta yi kiyasin cewa, karuwar GDP na shekarar 2014 za ta kai kimanin kashi 7.5 bisa dari, inda tattalin arzikin kasar zai samu bunkasuwa yadda ya kamata, abin da ya dace da tsarin da aka kayyade. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China