Ofishin nazari kan hasashe na kwalejin nazarin kimiyya a fannin zamantakewar al'umma na kasar Sin ya bayar da wani rahoto dangane da hasashen da ya yi wa tattalin arzikin Sin, inda aka bayyana cewa, a farkon rabin shekara ta 2014, Sin za ta samu karuwar tattalin arziki da yawanta zai kai kashi 7.4 bisa dari, haka kuma yawanta zai kai kashi 7.7 bisa dari a karshen rabin shekarar da muke ciki, a duk shekara ta 2014 yawan karuwar tattalin arziki wato GDP zai kai kashi 7.6 bisa dari.
Rahoton yana kyautata zaton cewa, a shekara ta 2014 Sin za ta samu karuwar kayayyakin masarufi cikin sauri, kuma za ta samu karuwar zuba jari yadda ya kamata, an yi hasashen cewa, yawan karuwar jarin da kasar Sin za ta zuba kan kadarori zai kai kashi 20 bisa dari, wadda ta yi daidai da ta shekara ta 2013.(Danladi)