in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan ribar da kamfanoni mallakar gwamnatin tsakiya ta kasar Sin suka samu zai kai kudin Sin yuan biliyan 1300
2013-12-29 16:15:23 cri
A ran 29 ga wata Mr. Huang Shuhe, mataimakin shugaban hukumar sa ido kan kadarori na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ce, kamfanoni da masana'antu mallakar gwamnatin tsakiya na kasar sun samu sakamako mai kyau a shekarar ta 2013, wato an yi hasashen cewa, yawan ribar da suka samu a shekarar bana zai kai kudin Sin yuan wajen biliyan 1300. Sakamakon haka, yawancin kamfanoni da masana'antu mallakar gwamnatin tsakiya sun cika kwangilolin da suka kulla da hukumar.

Mr. Huang ya fadi haka ne a yayin taron jarrabawa wadanda suke da nauyin tafiyar da manyan kamfanoni da masana'antu mallakar gwamnatin tsakiya na kasar.

Mr. Huang Shuhe ya kara da cewa, a tsakanin watan Janairu da na Nuwamba na bana, yawancin kamfanoni da masana'antu mallakar gwamnatin tsakiya sun samu kyautatuwa sosai wajen samun riba. Daga cikinsu, yawan ribar da kowane kamfani daga cikin kamfanoni 11 ya kai fiye da kudin Sin yuan biliyan 5. Wannan kyakkyawan sakamako ne da suka samu a cikin mawuyacin hali a lokacin da ake fuskantar yanayin tattalin arziki mai sarkakiya a cikin gidan, har ma a duk duniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China