in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bayyana tabbacin karuwar tattalin arzikin kasar
2014-01-22 10:37:02 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana tabbacin kasar cewa, tattalin arzikinta zai dore tare da bunkasa yadda ya kamata a wannan shekara ta hanyar aiwatar karin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje.

Mr. Li ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wani taron karawa juna sani da ma'aikata baki daga kasashen waje dake aiki a kasar sama da 70, inda ya ce, kasar Sin za ta iya ci gaba da samun sakamako mai kyau.

Alkaluma sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa da kashi 7.7 cikin 100 a shekara ta 2013, wato dai-dai da shekara 2012, inda ya dara hasashen da gwamnati ta yi na kashi 7.5 cikin 100.

Yawan kayayyakin da aka sayar a cikin gida ya kai kudin Sin kimanin Yuan Triliyan 5 kwatankwacin dala biliyan 826.4, kusan dai-dai da ci gaban alkaluman tattalin arzikin shekara-shekara na kasar.

Mr. Li ya ce, sakamakon radadin da ake fuskanta yayin da tattalin arzikin duniya ke farfadowa da kuma matsin lamba kan tattalin arzikin kasar Sin a shekarar da ta gabata, ya sa kasar Sin ta kara daura damara don dai-dai ci gaban tattalin arzikinta, yin gyara da inganta manufofi, bullo da matakan kula da harkokin tattalin arzikin cikin gida.

Ya ce, kasar za ta yi kokarin bullo da hanyoyin dogaro da kai, dauko kwararru daga ketare, ta yadda za su bayar da tasu gudummawar wajen yayata manufofinta na yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje.

Firaministan ya kuma yi amfani da wannan dama, wajen mika gaisuwar murnar sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa ga baki 'yan kasashen waje da ke aiki a nan kasar Sin da kuma iyalansu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China