in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasashen Larabawa
2013-12-22 17:02:03 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Aljeriya Ramtane Lamamra sun jagoranci wani taron manema labaru na hadin gwiwa a Asaba ran 21 ga wata a birnin Alger hedkwatar kasar Aljeriya, inda Mista Wang ya bayyana manufar da Sin take dauka kan kasashen Larabawa bisa sabon halin da ake ciki yanzu.

Mista Wang ya ce, Sin ta nace ga dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasashen Larabawa bisa hangen nesa. A cikin sabon halin da ake ciki, manufar da Sin take dauka kan kasashen Larabawa na kunshe da matakai hudu, na farko shi ne nuna goyon baya ga manufofin da kasashen Larabawa za su dauka. Sin na fahimtar bukatun 'yan Larabawa na yin kwaskwarima, kuma tana fatan kasashen Larabawa zasu fitar da wata hanyar da ta dace da halin da suke ciki da tsaron siyasarsu wajen neman samun bunkasuwa. Na biyu kuma, goyon baya ga matakin siyasa da kasashen Larabawa suke dauka wajen warware manyan batutuwan yankunan dake jawo hankalin kasa da kasa, da nace ga warware rikici ta hanyar yin shawarwari, da nuna goyon baya kan kokarin da suke na wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya. A cewar Mista Wang, Sin za ta taka rawarta wajen sa kaimi ga warware wasu batutuwan dake jawo hankalin kasa da kasa ta hanyar siyasa. Na uku kuwa, nuna goyon baya ga hadin kai da suke yi tare da kasar Sin domin samun bunkasuwa tare. A cewar Mr Wang, bangarorin biyu na da makoma mai haske wajen yin hadin kai. Sin na fatan hada matakin farfado da al'ummar Sinawa da burin bunkasa al'ummar Larabawa cikin jituwa tare, sannan da kara hadin kai a fannoni daban-daban, ta yadda jama'ar bangarorin biyu zasu ci gajiya. Na karshe kuma na hudu, goyon baya ga matakin da kasashen Larabawa ke dauka na kiyaye moriyarsu yadda ya kamata. Kasashen Larabawa muhimman mambobi ne wajen wanzar da zaman lafiya a duniya. Sin na adawa da duk wani matakin da za a dauka da zai keta mutuncin kasahen Larabawa da sunan yaki da ta'addanci da hakkin Bil Adama da sauransu. Haka zalika, Sin na fatan daidaita wasu manyan batutuwan da kasashen Larabawa ta hanyar sulhu tsakaninsu, ta yadda za su kiyaye moriyarsu har ma da ta dukkan kasashen masu tasowa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China