in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ba ta da niyar yin kutse a Ukraine, in ji ministan harkokin wajen kasar
2014-03-30 17:49:48 cri

Ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergey Lavrov, ya bayanna cewa, Rasha ba ta da burin yiwa kasar Ukraine kutse, kana matsayin ta daidai yake da na kasashen yamma kan wannan batu. Tuni dai Mr. Lavrov, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Amurka John Kerry don gane da hakan.

Da yake Karin haske ga manema labaru, Lavrov ya bayyana cewa, Rasha ba za mamayi iyakar kasar Ukraine ba, tana kuma fatan kasar ta Ukraine za ta kwantar da halin ta, ta kuma goyi bayan bukatar hadin kai tsakanin bangarorin da wannan batu ya shafa, domin tabbatar da burin da aka sa gaba.

Ya ce abun farin ciki shi ne, kasancewar matsayin da Rasha ke kai na kama da na kasashen yamma. Inda koda a 'yan kwanakin baya ma sai da ya gana da takwaransa na kasar Amurka John Kerry a birnin Hague, inda suka tattauna kan wannan batu tare da sauran masu ruwa da tsaki na kasashen Jamus, da Faransa da dai sauransu, matakin da ya yi fatan zai bada damar aiwatar da wata shawara, wadda za a gabatarwa gwamnatin Ukraine.

Rahotanni sun bayyana cewa, a kwanakin baya, mukadashin ministan harkokin cikin gidan kasar Ukraine Arsen Avakov, ya bayyana cewa gwamnatin kasar, na shirin kawar da makamai daga hannun wadanda ke rike da su ba bisa ka'ida ba. Matakin da Rasha ta nuna gamsuwa da shi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China