Babban taron MDD karo na 68 ya zartas da wani kuduri dangane da batun Ukraine a ran 27 ga wata, inda ya yi alkawarin tabbatar da ikon mulki da cikakken yankin kasar ta Ukraine, sa'i daya kuma ya kalubalanci bangarorin daban-daban da wannan batu ya shafa su yi shawarwari a siyasance kai tsaye, ta yadda za a warware batu cikin lumana.
Haka kuma taron kan Ukraine ya kada kuri'u kan wani daftarin kuduri mai taken "Cikakken yankin kasar ta Ukraine" da kasashe da dama, ciki hadda Ukraine suka tsara. Bisa sakamakon da aka gabatar, kasashe 100 sun amince da shi, ciki hadda Amurka, Birtaniya, Faransa, Jamus da sauransu, yayin da kasashe 11 suka nuna rashin amincewa da shi, wato Rasha, Cuba, Korea ta Arewa, Venezuela da sauransu, ban da haka kuma, kasashe 58 sun janye daga zaben, kamar Sin, Brazil, Indiya, Afrka ta Kudu, Uzbekistan da sauransu. Bisa ka'idar taron, za a zartas da daftarin kuduri bisa rinjayen kuri'un da aka jefa, babu wata kasar za ta hawan kujerar ta ki.
Dadin dadawa, kudurin ya yi watsi da zaben raba gardama da aka yi a ran 16 ga wata a jamhuriyyar Crimea da birnin Sevastopol, a ganinsa, wannan mataki ba zai canja matsayinsu ba ko kadan. Wannan kuduri bai ambaci kasar Rasha ba.
Wakilin din din din kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya yi jawabi a taron cewa, batun Ukraine na da alaka da moriyar kasa da kasa, shi ya sa ya jawo hankalinsu, ya kamata, a warware wannan batu cikin daidaituwa. Kamata ya yi, bangarorin daban-daban su yi hakuri domin kaucewar tsanantar da halin da ake ciki yanzu, kuma a ci gaba da daidaita bambancin ra'ayi ta hanyar siyasa ko diplomasiyya bisa dokoki da shari'a. (Amina)