in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen Amurka da Rasha sun yi shawarwari kan rikicin Ukraine a birnin Paris
2014-03-31 11:03:57 cri

Babban sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, da ministan harkokin wajen Rasha Serguei Lavrov, sun gudanar da shawarwarin warware rikicin kasar Ukraine.

Duk da dai ba a fayyace ainihin abin da suka tattauna yayin ganawar tasu a birnin Paris a jiya Lahadi ba, kafofin watsa labarun Faransa sun ruwaito cewa, shawarwarinsu suna da alaka da tattauna shawarwar da Rasha ta gabatar a baya, wato batun mayar da Ukraine bisa tsarin tarayya, don shawo kan matsalar da kasar ta fada.

Tun da fari kafin ganawar tasu, sai da Mr. Lavrov ya bayyana shawarar da Rashan ke ganin ta dace a bi wajen daidaita rikicin kasar ta Ukraine, wadda ke kunshe da baiwa yankunan kasar karin ikon tafiyar da harkokin su, bisa tsari na tarayya.

A ranar Lahadin da ta gabata ma daidai da Lavrov ya bayyana a kan shafinsa na Twitter cewa, muddin kasashen yammacin duniya sun amince da sauyin da aka samu a birnin Kiev helkwatar kasar ta Ukraine, to kamata ya yi su amince da matsayin yankin Crimea na komawa karkashin kasar Rasha.

Game da wannan batu, Kerry ya bayyana cewa, kamata ya yi Rasha ta janye sojojinta, da ta jibge a kan iyakar kasar Ukraine, ta kuma yarda da shawarwar tura masu sa ido na kasashen duniya, domin nazartar halin da ake ciki a kasar ta Ukraine. Haka zalika Kerry ya bukaci Moscow ta gudanar da shawarwari kai tsaye da Kiev, ta kuma girmama babban zaben shugaban kasar da ake fatan gudanarwa a ranar 25 ga watan Mayu mai zuwa.

Rahotannin baya bayan nan dai na nuna cewa, ana sa ran ganawar ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius, da takwaransa na Rasha a Litinin din nan. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China