Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fidda wani rahoto a ran 11 ga wata, wanda ke cewa, ma'aunin yawan sayayya na CPI da aka lissafta a watan Maris na bana ya karu da kashi 2.4 cikin dari bisa na bara war haka.
Hakan ya nuna cewa, adadin ya karu da kaso 2.3 bisa dari, idan an kwatanta shi da na bara war haka. Wani masani na ganin cewa, yanzu babu wani matsi mai tsanani da zai haddasa hauhawar farashin kayayyaki a kasar Sin. (Amina)