Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar da kididdiga a yau Litinin 14 ga wata cewa,wannan shi ne karo na farko da ma'aunin yawan sayayya wato CPI ya karu fiye da kashi 3 bisa dari bisa na makamacin lokaci na baya, tun bayan watan Fabrairu na bana.
Alkaluman sun nuna cewa, farashin kayayyakin zaman rayuwa guda 8 da aka saya a watan Satumba da ya gabata, farashin abinci ya haura da kashi 6.1 bisa dari.
Ban da haka, bisa kididdigar da aka samar, ma'aunin PPI ya ragu da kashi 1.3 cikin dari bisa na bara war haka, wanda bai kai na watan Agusta ba. (Amina)