in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan CPI na kasar Sin a watan Maris ya karu da kashi 3.6 cikin dari
2012-04-09 11:05:44 cri

Bisa alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayar a ran 9 ga wata, an ce, a watan Maris na bana, yawan CPI, wato ma'aunin farashin kayayyaki na kasar Sin ya karu da kashi 3.6 cikin dari bisa na makamancin lokacin shekarar bara, kuma wanda ya karu da kashi 0.2 cikin dari bisa na watan da ya gabata.

A hakika dai, farashin abinci ya karu da kashi 7.5 cikin dari, a sakamakon haka, yawan CPI ya karu da kashi 2.39. Kana, abincin da farashinsu ya karu sosai su ne nama da kayayyakin lambu, wadanda farashinsu ya karu da kashi 6.1 cikin dari bisa na watan da ya gabata.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China