Haka kuma, farashin abinci ya ci gaba da karuwa, yayin da farashin gidajen kwana shi ma ya karu sosai.
Ban da wannan kuma, a watan Agusta, farashin aikin jinya da kayayyakin masarufi ya karu, sai dai kuma farashin sufuri da sadarwa ya yi daidai da na watan da ya gabata.
Bugu da kari, yawan CPI na kasar Sin ya karu da kashi 0.5 cikin 100 bisa na watan da ya gabata. Sannan, daga watan Janairu zuwa watan Agusta, matsaikacin yawan farashin kayayyakin da masana'antu suka kera ya ragu da kashi 2.2 cikin 100 bisa na makamancin lokaci na bara.(Bako)