Wata jami'ar da ke aiki a hukumar kididdigar Yu Qiumei ta bayyana cewa, dalilin da ya sanya saurin karuwar CPI a watan Disamban bara, shi ne sabo da farashin abinci ya karu, musamman ma farashin kayan lambu.
Yu Qiumei ta ce, sakamakon yanayin sanyi, da dusar kankara, tare kuma da bikin gargajiya na Sinawa dake karatowa, farashin abinci zai ci gaba da tangal-tangal, amma bayan kammalar bikin, tare da karuwar yanayin zafi, irin wannan hauhawar farashin abinci zai ragu.(Bako)