in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Farashin kayayyaki a kasuwanni CPI ya karu da kashi 4,2 cikin 100 a watan Nuwamba
2011-12-09 16:50:53 cri

Ma'aunin farashin kayayyaki a kasuwanni CPI na kasar Sin dake a matsayin babbar hanyar shaida hauhawar farashin kayayyaki ya karu a cikin watan Nuwamba da kashi 4,2 cikin 100 a rinjayen shekara a yayin da yake da kashi 5,5 a cikin watan Oktoba, kamar yadda cibiyar kididdiga ta kasa BES ta bayyana a ranar Jumma'a.

CPI ya karu da kadan a cikin watan Nuwamba tun daga watan Oktoban shekarar 2012 a cewar cibiyar BES.

Farashin zaman rayuwa ya ragu da kashi 0,2 cikin 100 a cikin watan Nuwamba a rinjayen wata kamar yadda BES ta bayyana a cikin wata sanarwa data fitar ta shafin intanet.

Daga watan Janairu zuwa watan Nuwamba, CPI ya haura da kashi 5,5 cikin 100 bisa shekara guda, wanda ya wuce muradin kashi 4 cikin 100 na karon farko da gwamnatin kasar ta shirya na shekarar 2011.

Farashin kayayyakin abinci, bisa kashi daya cikin kashi ukku na ma'aunin kayayyaki a cikin kidayar CPI na kasa, sun samu karuwa da kashi 8,8 a watan Nuwamba a rinjayen shekara amma kuma sun fado kasa da kashi 0,8 cikin 100 idan aka kwatanta da na watan Oktoba a cewar BES.

Kafin wannan sanarwa ta BES, yawancin masanan harakokin tattalin arziki sun yi tsamanin karuwar shekara da kashi 4,2 zuwa kashi 4,4 cikin 100 na CPI a watan Nuwamba.

CPI na kasar Sin ya cimma kashi 6,5 cikin 100 a watan Yuli, wanda kai matsayin kula a watanni 37.

Farashin kayayyaki daga wajen sarrafasu IPP na kasar Sin, wata babbar hanya ce dake shaida hauhawa kayayyaki daga inda ake sarinsu dama ya karu da kashi 2,7 cikin 100 a watan Nuwamba bisa shekara guda.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China