Karuwar CPI na Sin ya ragu da kashi 2 bisa dari a watan Janairu
Bisa labarin da hukumar kididdiga ta Sin ta bayar ran 8 ga wata, an ce, a watan Janairu, ma'aunin farashin kayan masarufi wato CPI na Sin, ya karu da kashi 2 bisa dari, idan aka kwatanta na makamancin lokacin shekarar bara, inda yawan karuwarsa ya ragu da kashi 0.5 bisa dari bisa na adadin watan da ya wuce.
Bisa binciken da wata kwararriya a sashen kididdiga na hukumar ta yi, a watan Janairu, hauhawar farashin ganyaye da kuma nama ya yi tashin gwauro zabi a kasar Sin.
Bugu da kari, bisa kididdigar da aka yi, a watan Janairu, farashin abinci a Sin, ya karu da kashi 2.9 bisa dari, amma kudaden da jama'ar kasar suka kashe wajen tafiye-tafiye da kuma sadarwa ya ragu da kashi 0.3 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.(Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku