Tun farkon wannan shekara, yawan karuwar CPI da aka samu ya ci gaba da raguwa, wato adadin ya ragu daga kashi 4.5 cikin 100 a watan Janairu zuwa kashi 1.7 cikin 100 a watan Oktoba. Haka kuma yawan karuwar CPI da aka samu a watan Oktoba shi ne mafi kankanta a cikin wannan shekara, amma daga watan Janairu zuwa watan Oktoba, yawan matsakaicin karuwar CPI da aka samu ya kai kashi 2.7 cikin 100 bisa na makamancin lokaci na bara a duk kasar Sin.
A kuma bangaren farashin kayayyaki da masana'antu suka kera wato PPI, an ce, a watan Oktoba, yawan PPI din na kasar Sin ya ragu da kashi 2.8 cikin 100 bisa na makamancin lokaci na bara, kuma yawan raguwar da aka samu shi ma ya yi kasa bisa na watan Satumba da ya gabata. (Bako)