Bisa kididdigar da aka samu, ana iya gano tasirin da canjin farashi ya haifar, wato a watan Yuni, yawan alkaluman CPI ya ragu da kashi 0.6 cikin 100 bisa na watan jiya, haka kuma idan aka kwatanta farashin abinci, za a ga cewa, farashin kayan lambu ya ragu sosai .
Bugu da kari kuma, farashin kayayyakin da masana'antu suka samar wato PPI ya ragu da kashi 2.1 cikin 100 bisa na bara. A farkon rabin shekarar bana, yawan alkaluman PPI ya ragu da kashi 0.6 cikin 100 bisa na bara.(Bako)