Alkalumman na Disamban ya nuna za'a samu gejin hauhawar farashin ,inda zai tashi da kashi 2.5 a cikin 100 a shekara abin da ya yi kasa idan an kwatanta da kashi 3 a cikin 100 na watan nuwanban bana a cewar hukumar kididdiga ta kasar.
Kwararru a wannan fannin sun hakikance cewa faduwar alkalumman na CPI da kuma madaidaicin hauhawar farashi zai ba da dama ga mahukunta su cigaba da maida hankali a kan tsare-tsare da za su taimakawa ci gaban tattalin arziki da kokarin aiwatar da wasu gyare-gyare kan tsarin tattalin arzikin kasar a wannan shekarar. (Fatimah Jibril)