in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alkaluman CPI na Sin na watan janairu ya karu da 2.5%
2014-02-14 16:56:24 cri
Hukumar kididdiga ta Sin ta gabatar da wani rahoto a yau Jumma'a 14 ga wata cewa, a watan Janairu na bana,alkaluman CPI wato ma'aunin farashin kayayyaki na Sin ya karu da kashi 2.5 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, kuma karuwar da aka samu ta yi daidai da ta watan Disamba na bara.

Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, farashin abinci ya karu da kashi 3.7 cikin dari a watan Janairu na bana, wanda ya yi tasiri ga karuwar CPI da kashi 1.23 cikin dari.

Babbar jami'ar kididdiga ta sashin kula da birane ta hukumar kididdiga ta Sin, Yu Qiumei ta yi bayanin cewa, a watan Janairu na bana, farashin abinci ya karu sosai sabo da bikin sabuwar shekara.

A nasa bangare, mataimakin shugaban hukumar nazari da ba da shawara ta cibiyar mu'amalar tattalin arziki da kasashen waje ta Sin, Wang Jun ya furta cewa, ta la'akari da yanayin da ake ciki a watan Janairu, da halin bunkasar tattalin arziki, watakila farashin kayayyaki ba zai karu sosai a tsawon shekarar da ake ciki ba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China