Alhamis 9 ga wata, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar da rahoton cewa, ma'aunin yawan sayayya (CPI) na kasar Sin a watan Jarairu ya karu da kashi 4.5 cikin 100 bisa na makamancin lokaci na bara, kuma saurin karuwarsa ya karu da kashi 0.4 cikin 100 bisa na watan Disamba na bara.
Farashin abinci ya karu a watan Jarairun bana, saboda bikin ranar sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin. A cikin wannan wata, farashin abinci ya karu da kashi 10.5 cikin 100 bisa na makamancin lokaci na bara, kuma saurin karuwarsa ya karu da kashi 1.4 cikin 100 bisa na watan da ya gabata.(Amina)