in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da wakilan kamfanonin dake halartar dandalin Bo'ao na shekarar 2014
2014-04-11 10:27:29 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da wakilan shahararrun kamfanonin kasa da kasa, da ke halartar dandalin Bo'ao na shekarar 2014 a yammacin jiya Alhamis. Inda ya bayyana cewa, a kokarinta Sin na zurfafa yin kwaskwarima, da bude kofa ga kasashen waje, Sin za ta samarwa kamfanonin kasashen waje da suka yi rajista a nan kasar Sin wani yanayi mai kyau na yin takara cikin adalci.

Har wa yau, Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga raya sha'anonin kiyaye muhalli, musamman samar da tsabtacaccen makamashi, da rage fitar da gurbatacciyar iska, da tsimin makamashi, tare da fatan wadannan kamfanoni za su yi hadin kai da kamfanonin kasar Sin, tare da yin musayar ra'ayoyi kan kimiyya da fasaha bisa burinsu. Bugu da kari, firaministan kasar ta Sin ya ce, kasarsa za ta ci gaba da kiyaye ikon mallakar fasaha.

A nasu bangare, wakilan kamfanoni sun nuna cewa, bunkasar wannan dandali ta nuna babban ci gaban da Sin ta samu. Hakan ya sa kamfanonin kasashe daban-daban na kyautata tsare-tsarensu domin biyan bukatun bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin. Kuma wadannan kamfanoni mallakar wasu kasashe, za su kara zuba jari a kasar Sin, da habaka ayyukansu, har ma da kara yin hadin gwiwa da kawo moriyar juna. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China