Sakatare janar na taron tattaunawar Zhou Wenzhong ya bayyana cewa, taron ya jawo hankalin kasashen Asiya sosai musamman ma 'yan kasuwa na nahiyar, hakan ya sa shugabannin kasashen duniya, da 'yan kasuwa da kwararru, da manema labaru fiye da 2000 sun halarci taron. Mr. Zhou ya ci gaba da cewa, a yayin taron, wakilai mahalartar taron sun cimma daidaito a fannonin da aka dora muhimmanci sosai a kai, bisa taken taron, hakan an aza hasashe mai kyau wajen inganta hadin gwiwa da ke tsakaninsu.
Mahalartar taron da dama sun bayyana cewa, raya kasashen Asiya da suke amincewar juna da hadin gwiwarsu cikin aminci don samun bunkasuwa tare, ba ma kawai ya dace da moriyar kasashen Asiya tare, hatta ma zai taimaka wajen farfado da tattalin arziki na duniya da raya tsarin siyasa a tsakanin kasa da kasa yadda ya kamata.(Bako)