Duk da cewa, ranar ta fado a karshen mako, masu gabatar da kara da lauyoyin da ke kare shi sun amince a ci gaba da sauroron karar.
A ranar Alhamis ne kotun da ke Jinan lardin Shandong a gabashin kasar Sin ta fara sauraron karar bisa zargin da ake masa na karbar cin hanci, rashawa da kuma amfani da matsayinsa ta hanyar da ta saba wa doka.
Ana zargin Bo Xilai dan shekaru 64 da haihuwa da karbar cin hancin da ya kai Yuan miliyan 21.8 kimanin dala miliyan 3,5 daga hannun wasu 'yan kasuwa biyu, wato Tang Xiaolin da Xu Ming da almubazzaranci da dukiyar jama'a.
Ko da yake Mr. Bo ya musanta karbar cin hancin da sauran zargin da ake yi masa a lokacin da ake sauraron karar, kuma kotun ta amince da rokon da ya gabatar, wanda ya kasance cikin koshin lafiya a lokacin sauraron karar domin ya kare kansa.(Ibrahim)