Mai gabatar da kara na ganin cewa, ya kamata a yanke wa Bo Xilai hukunci bisa munanan laifuffukan da ya aikata na cin hanci da karbar rashawa da kuma yin amfani da mukaninsa ta hanyar da ba ta dace ba.
A kotun kuma, Bo Xilai ya yi karin bayani kan tuhumar da ake yi masa dangane da cin hanci, ya kuma musunta zargin da aka yi masa. Sa'an nan an yi bincike kan ko Bo Xilai ya karbi cin hanci ko a'a a kotun, inda masu gabatar da karar da lauyoyi masu kare Bo Xilai suka tambayi Bo Xilai da wani mai ba da shaida, masu gabatar da karar sun kuma gabatar da abubuwan shaida, bangarorin 2 sun tabbatar da shaidun da suka gabatar. Har wa yau Bo Xilai da lauyoyin da ke kare shi sun samu iznin bayyana ra'ayoyinsu a kotun.
A yayin da ake sauraron karar, Bo Xilai ya kasance cikin kwanciyar hankali da koshin lafiya.
An saurari karar yadda ya kamata, kuma da misalin karfe 6 na yamma an sanar da dage sauraron karar zuwa gobe Jumma'a ranar 23 ga wata. (Tasallah)