in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar harkokin Asiya a birnin Bo'ao
2014-04-08 15:35:59 cri

A Talatar ran ne aka bude taron shekara-shekara, na dandalin tattaunawar harkokin Asiya a birnin Bo'ao. Yayin bikin bude taron, firaministan Sin Mista Li Keqiang, da sauran shugabannin Sin da na waje, da yawansu ya kai kimanin 10, sun halarci taron bisa gayyatar da aka yi musu.

Babban taken wannan taro shi ne, 'sabuwar makomar Asiya, neman sabon karfi da ka iya habaka bunkasuwa'. A yanayin da ake ciki na raguwar saurin karuwar tattalin arzikin manyan kasashen Asiya, ana fatan tattauna yadda za a kara hadin gwiwa a fannin tattalin arziki, da dunkulewar kasashen wuri guda a wannan karo.

A 'yan kwanakin baya, babban sakataren dandalin Mista Zhou Wenzhong ya bayyana cewa a nan gaba, dandalin zai kara kokarin samar da wata kafa ta ba da hidima ga kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki domin habaka hadin kansu, za a kuma kara mai da hankali ga batun hadin kan na su, da bunkasuwarsu, da daga matsayinsu a duk duniya. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China