Yayin da take zartas da wannan hukunci kan Mr. Bo a yau Lahadin nan, Kotun ta bada umarnin kwace dukkanin dukiyar da ya mallaka, tare da haramta masa shiga dukkanin wasu harkokin da suka jibanci siyasar kasar.
Da take tabbatar da dalilanta na yanke wannan tsattsauran hukunci kan wannan tsohon jami'in gwamnati, kotun ta bayyana cewa kudaden da Bo ya karba kai tsaye, da wanda iyalinsa suka karba a matsayin na goro, sun kai kimanin dalar Amurka miliyan 3, da dubu dari 3.
Har ila yau an bayyana cewa tsakanin shekarun 1999 zuwa 2012, Bo, ya yi amfani da mukamansa a lokuta daban daban, da suka hada da magajin garin Dalian, da mukamin sakataren kwamitin jam'iyyar yankin, da gwamnan lardin Liaoning, da ma lokacin da yake matsayin ministan cinikayyar kasar, wajen nemawa wasu na hannun damarsa alfarma ta haramtacciyar hanya. (Saminu Alhassan Usman)