A ranar 16 ga wata, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi jawabi a gidan telebijin na kasar cewa, ya zuwa wannan lokaci, ba a tabbatar da su waye masu kulla makircin fashewar bom, da hujjar da ta sa su aikata wannan laifi ba, sannan kuma ba a sani ba, ko fashewar bom din na da alaka da ta'addanci da aka shirya a gida, ko wajen kasar da Amurka ba, amma, hukumar bincike ta tarayyar Amurka na kallom batun, bisa laifin ta'addanci, sabo da dukkan fashewar bom da aka kai ga jama'a ya zama laifin ta'addanci, ban da wannan kuma, Obama ya riga ya bukaci hukumomin da abin ya shafa, da su bi bahasin lamarin, don gurfanar da masu laifi gaban kuliya.(Bako)