in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun koli ta lardin Shandong ta kiyaye hukuncin karo na farko da aka yanke a kan Bo Xilai
2013-10-25 15:50:33 cri

A safiyar ranar Juma'a ta nan 25 ga wata, kotun koli ta lardin Shandong na mkasar Sin ta hukunta Bo Xilai a karo na biyu bisa laifuffukan cin hanci da rashawa, da amfani da ikonsa ba bisa doka ba, inda kotun ta yanke shawara cewa, bata amine da karar da Bo ya kai a kotun koli ba, kuma ta tsaya kan hukuncin daurin rai da rai da aka yanke masa a karo na farko.

Game da laifuffukan cin hanci da rashawa da amfani da ikonsa ba bisa doka ba da Bo Xilai yayi, kotu ta tsakiya ta birnin Jinan ta yanke hukunci a ranar 22 ga watan jiya, abinda yasa, Mr Bo ya daukaka kara, sa'an nan kotun koli ta lardin Shandong ya karbi shari'ar, kuma ta kafa tawagar alkalai don sake duddubawa.

Tawagar tana ganin cewa, dalilan da Bo Xilai da kuma masu kare masa suka gabatar ba hakikanan abubuwa bane kuma ba su da cikakkun shaida bisa doka, don haka ba za a iya amincewa da su ba.

Bisa ga abubuwan da aka tanada a cikin sashe na farko na rukuni na farko na babi na 225 a cikin dokar tuhumar masu manyan laifuffuka ta Jamhuriyar Jama'ar Sin, kotun koli ta ki saurarar karar da ya gabatar, kuma ta daukaka hukuncin da aka yanke masa a karo na farko. Kuma wannan hukuncin karo na biyu shine hukuncin karshe da aka yanke masa.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China