Shugaba Sata ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance wata abokiyar arzikin kasar Zambia tun tsahon lokaci, kuma a halin yanzu, kasar Sin na da kyakkyawan yanayin tattalin arziki, kasuwannin zuba jari, da kuma fasahohi na zamani. Don haka kasar Zambia na fatan kamfanonin kasar Sin, za su kara zuba jari a kasar, don bunkasa hadin gwiwar bangarorin biyu bisa fannoni daban daban.
Shugaba Michael Chilufya Sata ya kai ziyarar aiki a kasar Sin, ya kuma halarci taron dandalin tattaunawa na Bo'ao na Asiya na shekarar 2013 tun ranar 4 zuwa ta 11 ga watan Afrilu, bisa gayyatar shugaban kasar Sin Xi Jinping. Kuma wannan shi ne ziyarar aiki ta farko da shugaba Sata ya kai kasar ta Sin tun lokacin da ya hau ragamar mulki a shekarar 2011. (Maryam)