in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya yi shawarwari tare da takwaransa na Namibiya
2014-04-09 15:43:44 cri

Firaministan kasar Sin Mista Li Keqiang ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Namibiya Hage Geingob a birnin Sanya da ke lardin Hainan a ranar 9 ga wata da safe.

A ganawarsu, Mista Li ya ce, a matsayin kasar Afirka daya tilo da ta halarci taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan harkokin Asiya na wannan shekara, kasar Namibiya ta wakilci nahiyar Afirka dake saurin samun bunkasuwa. Kasar Sin tana mai da hankali sosai kan dangantakar da ke tsakaninta da Afirka, za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasashen Afirka bisa hanyoyin da suka dace da hakikanin halin da suke ciki wajen samun bunkasuwa. A nan gaba ba da dadewa ba shi mista Li zai kai ziyara a nahiyar Afirka da zummar kara ciyar da dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika gaba.

Geingob ya ce, kasar Sin tana kasancewa wata abokiyar kasar Namibiya bisa ko wane irin yanayin duniya. Namibiya na sanya alheri ga zurfafa hadin kai tsakaninta da kasar Sin. Ya ce, kasashen Afirka sun nuna goyon baya ga inganta hadin kai a tsakanin Afirka da Sin bisa tsarin hadin kai tsakanin yankunan biyu, ya yi imani cewa, ziyarar Li a Afirka za ta kara daga dangantakar da ke tsakanin Afirka da Sin zuwa wani sabon matsayi. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China