in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Senegal ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin
2014-01-11 16:45:26 cri

Shugaban kasar Senegal Machy Sall ya gana da Ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi wanda ke ziyara a kasar a ran jumma'an nan 10 ga wata.

Yayin ganawar, Mr Sall ya bayyana cewa, Sin abokiyar nahiyar Afrika ce wadda take goyon bayan kasashen Afrika sosai waje samun 'yancin kai, a yanzu haka kuma, hanyar da Sin take bi ta zama abin koyi ne ga kasashen Afrika wajen samun bunkasuwa, bugu da kari, taimakon da Sin za ta bayar nan gaba zai zama muhimmin mataki ne ga nahiyar Afrika wajen farfado da nahiyar.

Bayan da kasashen biyu suka maido da dangantakar su, a cewar shugaban, kasar Senegal ta sami taimako sosai daga kasar Sin, haka kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta kai wani sabon matsayi. Ban da haka, Senegal na fatan kara kulla aminci da hadin gwiwa tsakaninsu a fannin manyan ababen more rayuwa da kara bunkasa dangantakar abokantaka tsakaninsu.

A nasa bangare, Mr Wang Yi ya ce, Senegal muhimmiyar abokiyar kasar Sin ce a yammacin Afrika, don haka Sin na fatan mai da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta zama abin koyi ne ga sauran kasashe a Afrika bisa tsarin sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare.

Mr Wang yace ya kamata kasashen biyu su kare moriyarsu tare duk da sauyin halin da duniya za ta fuskanta, ita kuma Sin na fatan kara hadin kai da kasar Senegal a dukkan fannoni, da kuma kara taimakawa kasar wajen samun bunkasuwa da karfin kanta. Yana mai jaddada cewa a har kullum kasar Sin sahihiyar abokiyar kasashen Afrika ce ciki hadda Senegal har abada.

Daga baya kuma, firaministan kasar Senegal Aminata Toure ita ma ta gana da Wang Yi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China