Ministan al'adu na kasar Senegal Abdou Aziz Mbaye, da ministan kula da harkokin wasannin motsa jiki na kasar Mbagnick Ndiaye, da jakadan Sin da ke kasar Senegal Xia Huang, da mataimakin shugaban kungiyar wasan Kongfu ta Sin He Qinglong sun halarci bikin.
Ministan al'adu na Senegal Mbaye, ya yi babban yabo game da rawar da kasar Sin take takawa, wajen hadin gwiwa da mu'amala daga fannoni daban-daban a tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa, zuwan kungiyar wasannin kongfu ta Sin kasar Senegal ya zama shaida ga dankon zumunci da ke tsakanin kasashen biyu.
Shi kuma, a nasa bangare, ministan da ke kula da harkokin wasanni na Senegal Ndiaye, cewa ya yi, wasan kongfu na Sin ya yi babban tasiri a kasar Senegal, kuma Senegal za ta yi amfani da wannan dama don yada wasannin a sassan kasar.
Da yake maida jawabi, jakadan kasar Sin da ke kasar Senegal Xia Huang ya ce, ainihin ma'anar wasannin kongfu ita ce, samar da zaman lafiya, haka kuma wasannin Kongfu ya nuna wayewar kan Sinawa cikin shekaru dubu 5 da suka gabata. Yana fatan yin amfani da wannan dama, don yada al'adu na Sinawa, da kara yin mu'amalar al'adu da ke tsakanin kasashen biyu.(Bako)