in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Senegal ya kammala ziyarar aiki a Burkina-Faso
2013-07-23 10:22:43 cri
Shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya kawo karshen wani rangandinsa na farko a matsayinsa na shugaban kasa a ranar Litinin a kasar Burkina-Faso. Shugaban na Senegal ya isa kasar Burkina-Faso a ranar 20 ga watan Yuli a karkashin wata babbar tawaga. Mista Macky Sall ya samu tattaunawa tare da takwaransa na Burkina-Faso Blaise Compaore kan batutuwa habaka huldar dangantakata ta moriyar juna tsakanin kasashen biyu, a cewar wata sanarwar hadin gwiwa da aka bayar bayan kammala wannan ziyara. Haka kuma shugabannin biyu sun nuna yabo kan muhimmiyar dangantakar dake tsakanin Senegal da Burkina-Faso tare kuma da bayyana bukatarsu ta ganin an shirya wani taron kwamitin hadin gwiwa na dangantaka a wajen karshen watanni uku na shekarar 2013 a kasar Burkina-Faso. Shugabannin biyu sun kuma jaddada niyyarsu ta siyasa domin kara aiwatar da manufar dunkulewar shiyyarsu da ma nahiyar Afrika da ta fi daukar hankalin manyan jama'an biyu musammun ma bisa la'akari da cigaban tattalin arziki da na al'umma na yammacin nahiyar Afrika, zaman lafiya, tsaro da kuma mulki na gari in ji wannan sanarwa. Hakazalika shugabannin kasashen biyu sun gamsu da halin da ake ciki a kasar Mali ta fuskar tsaro da zaman lafiya, tare da yin kira ga dukkan jam'iyyun siyasa na kasar dake cikin takarar zaben shugaban kasa na ranar 28 ga wata a kasar Mali tare da magoya bayansu da su yi iyakacin kokari domin ganin an gudanar da wannan zabe cikin yanayin zaman lafiya mai kyau. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China