"Ina godiya ga kasar Sin inda zan kai ziyara nan wata guda, ganin yadda wannan kasa ta taimaka sosai kan cigaban kiwon lafiya, tare da zuba kudi wajen wannan asibitin. Haka kuma ina isar da godiyata ga sauran jarin da wannan kasa ta zuba a fannonin noma, wasannin motsa jiki, al'adu da sauransu," in ji shugaba Macky Sall.
Shugaban Senegal ya yi wannan furuci a yayin bikin bude asibitin kananan yara dake garin Diamniadio mai tazarar kilomita 37 daga birnin Dakar da kasar Sin ta bai wa kasar Senegal bisa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
A makon da ya gabata, ministan harkokin wajen kasar Senegal Mankeur Ndiaye ya bayyana cewa kasarsa ta kafa muhimman ayyuka 23 tare da taimakon kasar Sin.
A cewarsa, wasu karin ayyuka goma sha hudu ana gudanar da su wadanda suka hada da gina filayen wasannin motsa jiki goma sha daya a cikin jihohin kasar, gidan al'adun bakar fata da kuma filin wasan kokowa.
Haka kuma shugaba Macky Sall ya bayyana cewa, ziyarar aikin da zai yi a kasar Sin a cikin watan Faburairu za ta kara fadada dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Senegal a muhimman fannonin da za su taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Senegal. (Maman Ada)