Cikin jawabin Amadou KANE, ya bayyana cewa kasar Sin, ta taka muhimmiyar rawa wajen raya zamantakewar al'umma, da tattalin arzikin kasar Senegal, kuma ayyukan da Sin ta taimakawa Senegal wajen wanzar da su, sun haifar da kyautatuwar rayuwar jama'ar kasar, tare da samar da hakikanin moriya mai yawa.
A nasa tsokaci, jakada Xia cewa ya yi kasar Sin, za ta ci gaba da kokartawa wajen ba da tallafi ga ayyukan raya kasar Senegal, don ci gaba da yalwata hadin gwiwar sada zumunta tsakanin bangarorin biyu.(Bako)