A gun bikin bude taron, shugaban karba-karba na kungiyar UEMOA na wannan karo, kuma shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé, ya bayyana cewa, mayar da batun samar da zaman lafiya da tsaro cikin tsarin tattaunawar kungiyar ta UEMOA, ya zama wata hanya daya tak da za a bi don cimma burin hadin gwiwar kasashen da ke yankin.
Daga nan sai ya yi kira ga kungiyar UEMOA, da ta gaggauta kafa tsarin ko-ta-kwana game da harkokin tsaro, tare da daukar hakikanin matakan cimma burin tabbatar da gudanar da harkokin tattalin arziki, da saka jari yadda ya kamata a tsakanin kasashe mambobin ta, duk kuwa da halin kunci da ake ciki a yankin.
A sa'i daya kuma, Faure ya yi maraba da farfado da tsarin mulki a kasar Mali, yana mai cewa kungiyar UEMOA na bukatar kasar Mali mai karfi da wadata, don samun nasarar aiwatar da shirye shiryen kungiyar da aka tsara. A sa'i daya kuma, ya yi kira ga bangarorin daban daban da su nuna goyon baya, game da yunkurin zabe a kasar Guinea-bissau, yana mai cewa kungiyar UEMOA, da kungiyar raya tattalin arziki ta yammacin Afrika wato ECOWAS, za su yi kai daya don taimakawa Guinea-bissau wajen shirya babban zabe.
Har ila yau Faure ya yi kira ga mambobin kungiyar ta UEMOA, da su dauki matakan da suka dace, don cimma burin karuwar tattalin arziki da kawo alheri ga jama'a.(Bako)