in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Senegal ta nuna yabo ga rukuni na 14 na kungiyar ba da aikin jinya ta kasar Sin
2013-09-05 14:51:11 cri
A ranar 4 ga wata, gwamnatin Senegal ta nuna yabo ga rukuni na 14 na kungiyar ba da aikin jinya da gwamnatin Sin ta tura zuwa kasar, da kuma irin nau'rorin ba da aikin jinya da Sin ta aika ga cibiyar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta kasashen Sin da Senegal.

Wakilin ministan kula da harkokin kiwon lafiya na kasar Senegal ya jinjina kyakkyawan aiki da fasahohi na kungiyar ba da aikin jinya ta kasar Sin, kuma ya nuna godiya ga gudummawar da suka bayar wajen taimakawa Senegal ta fuskar kyautata harkokin kiwon lafiya na kasar.

Karamin jakadan dake kula da harkokin tattalin arziki da kasuwanci na kasar Sin da ke kasar Senegal Huang Mingyuan ya bayyana cewa, kasar Sin tana dukufa ka'in da na'in wajen inganta hadin gwiwa da kasashe masu tasowa, kuma yana fatan kara kokari wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kyautata zaman rayuwar wadannan kasashe.

A cikin shekaru biyu da suka gabata, wannan kungiyar ba da aikin jinya ta Sin ta ba da aikin jinya ga mutanen da jimillarsu ta kai dubu 26, kuma ta kan shirya wasu ayyukan ba da aikin jinya a kyauta, abin da ya samu karbuwa a kasar. Yanzu, rukuni na 15 na kungiyar ba da aikin jinya karo na 15 ta kasar Sin ta riga ta isa kasar Senegal, kuma za su ci gaba da ba da hidimomi ga jama'ar kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China