Bisa labarin da gidan telebijin na TFM na kasar ya bayar, an ce, an yi garkuwa da mutanen 12 ne a wani wuri dake kudancin birnin Ziguinchor na yankin Casamance wanda kungiyar nakasassu ta duniya dake kasar ta mallaka, kuma dukkan mutanen 12 ma'aikata ne masu kawar da boma-bomai na kamfanin Mechem na kasar Afirka ta Kudu, a cikinsu hadda mata 3.
Manazarta sun yi hasashen cewa, watakila lamarin yin garkuwa da masu kawar da boma-boman yana da nasaba da ayyukan kungiyar demokuradiyya ta neman yankin Casamance, wadda ta taba kin amincewa da aikin kawar da boma-bomai a yankin na Casamance.
Tun daga shekarar 1982, an yi ta samun tashe-tashen hankali a yankin Casamance na kasar ta Senegal, wadanda suka haddasa mutuwar mutane fiye da dubu daya, baya ga mutane fiye da dubu 10 da suka rasa gidajensu. (Zainab)