Asusun ba da lamuni na kasa da kasa IMF ya sanar a ran 27 ga wata cewa, zai maido da ofishinsa a kasar Zimbabwe, kuma ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin IMF da Zimbabwe ta sami sassauci bayan hukumar ta janye daga kasar a tsawon shekaru 10 da suka gabata.
Ministan kudin kasar Zimbabwe Patrick Antony Chinamasa ya yi maraba da wannan mataki, tare da fatan ganin hadin kai tsakanin bangarorin biyu zai samun cigaba.
A shekarar 2002 ne, kasashen yammacin duniya suka garkamawa kasar ta Zimbabwe takunkumi. Bayan shekara daya, IMF ya dakatar da ikon kasar na kada kuri'u kan harkokin IMF, kuma ya janye ofishin wakilcinsa daga kasar a shekarar 2004. Kawo yanzu, bashin da IMF ke bin Zimbabwe ya kai miliyan 125, kuma kasar ta Zimbabwe ta kasa biya tukuna. (Amina)