in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Diyar shugaban Zimbabwe ta yi aure
2014-03-02 16:23:10 cri
Jiya Asabar daya ga wata, aka shirya wani gagarumin bikin aure ma Bona Mugabe diyar Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe , inda mutane sama da dubu 4 suka halarta ciki har da shugabannin kasashen Afirka da dama.

Ranar 21 ga wata, Robert Mugabe mai shekaru 90 a duniya ya yi bikin ranar haihuwar shi kansa sannan daga bisani, bayan mako guda diyar sa Bona ta yi aure.

An dai shirya wannan bikin bisa al'adun kasashen yammacin duniya a gidan Mugabe dake karkarar birnin Harare, hedkwatar kasar Zimbabwe.

Wadanda suka halarci wannan biki sun hada da shugabannin Zambiya, Afirka ta Kudu, Kongo Kinshasa da sauransu. Gidan talebijin kasar Zimbabwe ya gabatar da wannan biki kai tsaye inda aka bada labarin cewa an kashe kudin Amurka dala miliyan 5 domin shirya wannan bikin. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China