Kotun ta ce, an yi babban zaben kasar a ranar 31 ga watan Yuli cikin adalci kuma a bayyane, don haka ta amince da sakamakon zaben. Ban da wannan kuma, kotun ta yi watsi da karar da Morgan Tsvangirai ta kai gabanta, wadda ta nemi sake shirya babban zaben kasar. A sa'i daya kuma, kotun ta bayyana cewa, bayan da lauyoyin Tsvangirai suka gabatar da karar, sun yi jawabi dake nuna raini ga kotun, tare kuma da nuna shakku game da sahihancin hukunci da za ta yanke, don hakan, kotun ta ba da umurni ga hukumar gabatar da kara, da su gudanar da bincike kan wadannan lauyoyin biyu.
Douglas Mwonzora, kakakin jam'iyyar MDC da ke karkashin shugabancin Tsvangirai, ya nuna bakin ciki game da hukuncin da kotun ta yanke, kuma ya ce, jam'iyyar MDC za ta ci gaba da daukar mataka ta hanyoyin siyasa da diplomasiyya don sauya yanayin zabe da ta nuna shakku a kanta.(Bako)